Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Wani sabon zagaye na tsokana da gwamnatin Jamhuriyar Azerbaijan ke yi ga dabi'un mafi rinjayen Shi'a na wannan ƙasar a kwanakin nan ya juya zuwa mafi muhimmanci labari na zamantakewa a yankin da duniyar Islama. Ɗaukar sabbin dokoki kan sutura a makarantu, a daidai makonnin farko na shekarar karatu, ya hana ɗaruruwan ɗalibai mata da malamai masu hijabi halartar azuzuwan karatu. Wannan yanayi nan take ya samar da raɗaɗi a matakin yankin da duniya kuma ya kasance tare da martanin suka da dama.
Mafi muhimmanci martanin waje ya fito ne daga Turkiyya, ƙawa kuma abokiyar kuma abokiyar dabarun Jamhuriyar Azerbaijan. Oktay Saral, babban mashawarcin shugaban Turkiyya, ya ɗauki waɗannan ƙuntatawa a matsayin "abin da ba za a karɓa ba" kuma ya nemi Baku da ta "gyara kuskurenta nan take." Har ma Kemal Kılıçdaroğlu, shugaban babbar jam'iyyar zaman duniya da rashin addini ta Turkiyya wadda shi kan shi ke adawa da gwamnatin musulunci ta Erdogan ma ya nemi Azerbaijan kada ta maimaita kuskuren Turkiyya kan batun hijabi.
A wannan fanni al'ummar musulmi na Istanbul, birnin Turai na Turkiyya, sun taru a gaban ofishin jakadancin Jamhuriyar Azerbaijan a wannan birni kuma sun yi rera taken: "Hijabi, Asalin Mace Musulma Ce."
Mahmud Arikan, shugaban tsohuwar jam'iyyar Saadet ta Turkiyya ma, a cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa Ilham Aliyev, tare da tunatar da mummunan gogewar 28 ga Fabrairu a Turkiyya da juyin mulkin da aka yi a wannan ƙasar, ya kwatanta haramcin hijabi da "zurfin rauni a cikin lamiri."
Amma a gefe guda jam'iyyar da ke mulki ta "Sabuwar Azerbaijan" a Jamhuriyar Azerbaijan, ta mayar da martani ga waɗannan suka kuma tare da nanata yanayin zaman duniya na wannan ƙasar, ta roƙi hukumomin Turkiyya da kada su shiga cikin harkokin cikin gida na wannan ƙasar. Wannan jam'iyyar ta yi gargaɗi cewa amfani da batun hijabi a matsayin kayan aiki zai iya lalata dangantakar ɓangarorin biyu. A hakikanin gaskiya kamar Turkiyya, hukumomin Jamhuriyar Azerbaijan ma sun mayar wa Ankara amsa ta hanyar amfani da ƙarfin da ba na hukuma ba.
A duniyar Shi'a ma har zuwa wannan lokaci Sayyid Muqtada al-Sadr, shugaban ƙungiyar Sadr ta Iraki, ya yi Allah-wadai da matakan Jamhuriyar Azerbaijan wanda ya cancanci yabo. A Iran din musulunci ma wadda take da mafi kusancin addini da al'adu da al'ummar Jamhuriyar Azerbaijan har yanzu babu wani martani na hukuma ko wand aba na hukuma mai mahimmanci da ya faru.
Gaskiyar ita ce halin ƙiyayya na gwamnatin Ilham Aliyev a al'amuran da suka shafi Shi'anci da Iran, ya haifar da damuwa kan irin mu'amalar da wannan ƙasar za ta yi da gargaɗi daga Jamhuriyar musulunci a wurin wasu jami'an gwamnatin Iran.
A yanayin da Iran ke cikin wani babban yaƙi da Amurka da Isra'ila kuma Fadar White House tana bin siyasar killacewar teku da ƙasa na Iran kuma gwamnatin Baku sau da yawa ta nuna ƙiyayyarta ta hanyar rufe hanyoyin wucewa da jinkirta dubban motoci da direbobin Iran a bayan iyakoki; abu ne a hankalce cewa tsammanin mu'amala kai tsaye da ta hukuma ba abu na hankali ba sosai amma babu wani cikas ko la'akari ga martani na jama'a da na wanda ba hukuma ba.
Dangane da haka mafi kyawun mataki a wannan yanayi, shine goyon bayan jama'a da Shi'an ga buƙatar hijabi a Azerbaijan. Kamar yadda a cikin yaƙin Azerbaijan da Armenia wanda aka yi da iƙirarin sake kwace yankunan Azari, kusan dukkan da'irorin addini da zamantakewa masu alaƙa da batun kamar limaman Juma'a na biranen Iran masu yawan Turkawa da manyan mutane na Ardabil da lardunan Azerbaijan da har ma da Zanjan sun tallafa wa haƙƙin Jamhuriyar Azerbaijan. Har ma shahidin jagoran juyin juya hali a cikin wata maganarsa ya tallafa wa haƙƙin Jamhuriyar Azerbaijan kuma a lokaci guda ya tunatar da kiyaye haƙƙin Armeniyawa.
Yanzu ya dace ƙarfin jama'a a lardunan da ke kusa da Jamhuriyar Azerbaijan musamman Ardabil da Azerbaijan ta Gabas su shigo fagen su bayyana goyon bayansu ga haƙƙin Shi'an Azerbaijan. A wannan fanni rawar wasu limaman Juma'a ababen ƙauna a waɗannan yankuna tana da matuƙar mahimmanci waɗanda dole a tallafa musu. Gwamnatin Baku ta nuna cewa tana da matuƙar damuwa kan tasirin kalaman da shaharar manyan mutane na addini na Azari na Iran cikin Jamhuriyar Azerbaijan.
A fannin diflomasiyya bana hukuma ba, amfani da kyakkyawar dangantakar 'yar shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Dr. Pezeshkian da 'yar Ilham Aliyev waɗanda za su iya yin magana da harshen Azari da juna ana iya nazari a kai. Yar shugaban ƙasa mai daraja wanda ke aiki a matsayin mashawaci a ofishin shugaban ƙasa kuma daga cikin masu fafutuka a duniyar intanet zai iya da saƙo da harshen Azari da rubutun da ake amfani da shi a wannan ƙasar, ƙara wa Dr. Pezeshkian daraja.
A kowane hali ana iya samun tasiri mai inganci kan yanayin Shi'an Jamhuriyar Azerbaijan cikin hikima. Hukumomin Baku suna da ruɗani da damuwa mai yawa kan rawar Iran kuma har ma a cikin wannan rikicin hijabi suna ɗaukar Iran a matsayin mai haifar da matsalolinsu da shawarwarinsu kuma sun bayyana hakan a fakaice.
Ya kamata a sani cewa Jamhuriyar Azerbaijan da yukunrinta a kwanan nan ta sa ƙafa cikin wani kwatami da gwamnatoci mafi girma da ƙarfi fiye da ita a yankin suka taɓa sawa a baya amma ba su iya tsira daga gare shi ba.
..........................
Ra'ayinka